<?xml version="1.0" encoding="UTF-8"?><song><lyrics>[V1]
 1) Raina na ba da shi, na ba da jinina,
 Jin daɗi duk na ƙi saboda ƙaunarka.
 Raina na ba da shi, in ji Ubangiji,

[V2]
 2) Gidan Ubana can, gida mai daraja,
 Na fito don in zo in zama talaka.
 Na ba ka dukiyata, in ji Masoyinka.

[V3]
 3) Baƙunci mai wuya na haƙura da shi.
 Kewa da ƙishiruwa, yunwa, gajiya, na ji.
 Duk dominka na sha, in ji Mai Cetonka.

[V4]
 4) Ba za ka gane ba wahalar da na sha
 Domin in ba ka rai, rai na har abada.
 Da yardar rai na yi, in ji Maɗaukaki.

[V5]
 5) An fanshi naka rai da tamani mai yawa.
 Nan gaba za ka kai wasu gun giciye.
 Kai ne da nemansu, in ji Mai Cetonku.</lyrics>
<title>Raina Na Ba da Shi, Na Ba da Jinina LW85</title>
<hymn_number>85</hymn_number>
</song>